Ƴan arewa za su marawa na Kudu baya tarihi zai maimaita kansa – a cewar Ganduje.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewa, jihar Kano za ta maimaita abin da ya faru a zaben shugaban kasa na 1993 lokacin da jihar ta goyi bayan dan takarar Kudu tare da kin amincewa da dan jihar Kano.
Gwamnan ya ce hakan ya faru a baya sun zabi Cif MKO Abiola na jam’iyyar SDP kuma suka ki Bashir Othman Tofa na National Republican Convention (NRC), domin duk sun yi imani da haɗin kai da cancantar ƙasa.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar, sanarwar ta baayyana cewa, gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin wani rangadin yakin neman zabe tare da ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai daban-daban a babban zabe mai zuwa, yayin da ya ziyarci Hakimin Kibiya, Sunusi Abubakar Ila, bayan gudanar da taron yakin neman zabe da tuntubar juna a Rano da Bunkure kuma ya wuce Rano, hedkwatar masarautar Rano tare da tawagarsa.

Da yake tunatar da ‘yan Nijeriya cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya goyi bayan ‘yan Arewa a lokuta daban-daban domin samun nasarar lashe zaben.
Ya tunatar da cewa, Tinubu ya kasance makami ne wajen ganin Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Congress (AC), ya kuma samar wa Nuhu Ribadu wani dandali na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).
Da yake bayyana cewa, a matsayin karba-karba, takarar shugaban kasa a kasar, ya tanadi cewa, mulki na karba-karba ne daga Arewa zuwa Kudu da kuma akasin haka.
Gwamna Ganduje ya jaddada cewa, Tinubu, shi ne daya tilo da ya cancanta kuma mafi cancantar dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, Arewa ce ke goyon bayansa saboda akidarsa a kan gina kasa, wanda ya hada da kowa da kowa, cikakken imani da ci gaban dan Adam da kasa baki daya.
Ya gabatar da duk wasu ‘yan takarar da ke neman mukaman Sanata, dan majalisar wakilai na tarayya da dan majalisa na jiha, da Dakta Nasiru Yusif Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamna na mataimakinsa Murtala Sule Garo.