
Daga Abba Anwar
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin rattaba hannu ba tare da bata lokaci ba, ga kudurin nan da Majalisar Dokoki ta Jihar za ta turo masa kan bukatar samar da wasu sababbin Masarautu guda hudu daga masarautar Kano.

Ya bayyana hakan ne a yau Laraba a jawabi ga ‘yan jarida daf da fara zaman Majalisar Zartaswa ta jiha, a karo na 136, a gidan gwamnatin jihar Kano.

Ya ce sun samu labarin wata kungiya wadda ya bayyana da masu kishin jihar Kano, su ka kai bukatarsu ga Majalisar Jiha kan kara kirkiro wasu masarautu daga wadda a ke da ita yanzu.
Sai ya ce “A shirye nake da na rattaba hannu a wannan Kuduri da zarar Majalisa sun turo min ba tare da bata lokaci ba.” Masarautun da a ke bukatar kirkirowa kuwa sune, a Rano, Karaye, Bichi da Gaya.
Ya kara da kalubalen cewa ai duk mutumin da ya zo da wannan irin bukata an tabbatar ya na da tsananin kishin jama’ar jihar Kano din ne. Da kuma jihar gaba dayanta, kamar yadda ya nuna.
“Da zarar Majalisa ta gama yin duk abubuwan da za ta yi a kan wannan kuduri, kuma su ka kawo min, to ina mai tabbatarwa da al’umma cewar zan sa hannu kudurin ya zama Doka nan take ba tare da bata wani lokaci ba,” ya ce.
Sannan kuma ya tunasar da cewa dama ai tuntuni shekaru da yawan gaske da su ka wuce an so a samar da wasu masarautun daga cikin masarautar jihar Kano, amma Allah bai yi ba.
A dalilin haka ya ce sai yanzu Allah Ya kawo lokacin da wannan abu zai tabbata. “Ba za mu bata lokaci ba kuwa wajen tabbatuwar wannan aikin na ci gaba,” ya kara tabbatarwa.
Ya kara da cewa ya dau aniyar sa wa kudurin hannu ne ya zama doka, musamman ma saboda wannan wani abin alheri na wanda jama’ar Kano su ke maraba da shi. Kuma hakan a cewarsa zai kara samar da ci gaba mai dorewa ga wannan jiha.
“Akwai tabbacin za a samu ci gaba na gaske a dukkanin bangarorin wannan jiha ta mu mai albarka. Fatanmu ma shi ne kar abin ya ja wani lokaci,” in ji Gandujen.