Babban Bankin Najeriya CBN ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya bayyana cewa rashin wadatuwar sabbin kudaden da aka sauyawa fasali nada alaka da rashin takardun da ake buga kudin.

Musanta kalaman na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, inda ya ce Emefiele bai yi wannan furucin ba a gaban majilisar Kolin kasar wanda ya gudanar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce a yayin jawabin Emefiele ya shaidawa majalisar cewa kamfanin da ke aikin buga kudin na ci gaba da gudanar da aikin sa domin ganin ‘yan Najeriya sun wadata da sabbin kudaden.

Bankin ya ce hukumar da ke aikin lura da buga kudin na ta da wadatattun kayan aiki da take buga kudade.

Sanarwar ta bukaci da al’ummar kasar su yi watsi da rahotannin da su ke yawo cewa bankin bashi da wadatattun kayan aikin da zai buga sabbin kudade,tare da bai’wa mutane hakuri cewa su na ci gaba da aikin buga kudin domin su wadatar da al’ummar kasar baki daya.
Sannan akwai wani sakon murya da ya ke yawo a shafukan sada zumunta cewa CBN na yunkurin rufe wasu bankuna a kasar wanda hakan ba gaskiya ba ne.
Bankin ya bayyana cewa sakon muryar da aka fitar ya sabawa dokar tsarin bankin na CBN, tare da umartar mutane da su yi watsi da sakon muryar da ke yawo.