Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da cewar taa karbi isassun kuɗi daga bankin ƙasa da za ta gudanar da aikin zaɓe.

Kwamishinan zaɓe na ƙasa ne ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust hakan a daren da ya gabata.


Ya ce kwamishinonin zabe na jihohi za su karɓi isassun kuɗi daga bankin CBN na jihohinsu.
Hakan ya biyo bayan sabon tsarin babban bankin kasa CBN dangane da tsarin biyan kuɗi ta intanet.
Sai dai hukumar ta bukaci bankin ya bata kuɗi na takarda domin gudanar da zaɓen cikin tsari yadda ya kamata.
Shugaban hukumar na ƙasa Farfesa Mahmud Yakubu ne ya buƙaci hakan yayin da ya ziyarci gwamnan bankin dangane da sabon tsarin.
Bayan amincewa tare da fitar da takardun kuɗin da CBN ya yi, hulumar EFCC da ICPC za su sanya idanu a kan yadda hukumar za su kashe kudaɗen.