Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta haramta wa dukkan ma’aikatan da aka gano sun yi sakaci a zaben shugaban ƙasa da ‘yan majalisun tarayya daga shiga aikin zaben gwamnoni mai zuwa.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ne ya sanar da haka a wurin taronsa da kwamishinonin hukumar (REC) wanda ya gudana a Abuja yau Asabar.


Ya ce yayin da suke tunkarar zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokokin jihohi ya zama wajibi su ƙara zage dantse wajen magance kalubalen da suka fuskanta a zaben da ya gabata.
Dukkan ma’aikatan da aka gano suna da sakaci, ko waɗanda muka saba aiki da su ne ko masu aikin wucin gadi, ciki harda masu raba kaya da masu tattara sakamako, kada a saka su a zaɓe mai zuwa.
Kowane kwamishinan zabe (INEC) ya gaggauta ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wanda kwararan shaidu suka tabbatar ya tafka kuskure a zaben da ya gabata.
Yakubu ya bayyana cewa wannan taron shi ne karo na uku cikin watanni biyu kuma kamar kowane zama, sun tattauna batutuwan da suka shafi babban zaben 2023.
A cewarsa, sun ƙara nazari kan zaben shugaban kasa da ya wuce mako ɗaya nan baya da kuma zaben gwamnonin da ake tunkara nan da mako ɗaya ranar 11 ga watan Maris.
Shugaban INEC ya yaba da sadaukarwar yan Najeriya da kuma wayewa da fahimtar da jagororin siyasa suka nuna duk da banbanci inuwa a lokacin zaɓe.