Kotun koli ta tabbatar da sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin wanda ya lashe zaben Kano ta Tsakiya a madadin tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a a hukuncin da alkalai biyar su ka yanke karkashin jagorancin mai shari a Inyang Okoro.
A yayin yanke hukuncin kotun ta umarci hukumar zabe ta kasa INEC da ta maye gurbin sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin wanda ya lashe zaben a jam’iyyar NNPP a madadin malam Ibrahim Shekarau.

Kotun ta kuma tabbatar da halaccin hukuncin da kotun daukaka kara ta tabbatar da Hanga a matayin wanda ya ci zaben wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kotun Kolin ta bayyana cewa INEC ta yi kuskuren rashin cire sunan Malam Ibrahim Shekarau da ta sanya Sunan Hanga a matsayin dan takarar kujerar sanatan Kano ta Tsakiya bayan komawar Malam shekarau din jam’iyyar PDP.
Mai shari’a Emmanuel Agim a takardar hukuncin da ya karanto wacce mai shari’a Uwani Abba-Aji ta rubuta ta yi watsi da sunan Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kotun ta tabbatar da hukuncin kotunan biyu wanda babbar kotun tarayya da ta daukaka kara da ke Abuja su ka yanke ta tabbatar da Hanga a matsayin dan takarar Jam’iyyar ta NNPP a Kano ta Tsakiya.