Babban bankin Najeriya CBN har yanzu bai sakarwa bankuna tsoffin takardun kudi na Naira 1000 da 500 ba, duk kuwa da umarnin da ya bai wa bankunan na cigaba da rarraba su.

Hakan yana zuwa ne a tsaka da yadda bankunan suke ta fafutuka Dan ganin sun kara yawan wadatar da abokan huldarsu, wadanda suke tururuwa zuwa rassan bankunan a fadin jihohi da birnin tarayya Abuja.
‘Yan kasuwa, dalibai, masu na’urar cire kudi ta POS da sauransu da suka ziyarci bankunan, sun ce lamarin bai musu dadi ba sakamakon gaza cirar adadin kudin da suke bukata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda suka zanta da wakilansu sun ce, ana basu Naira dubu biyar da dubu goma ne kawai. Sai kuma ‘yan tsiraru da suke samun dubu Ashirin da ‘kyar.

Ranar Litinin din da ta gabata, CBN ta bakin mai magana da yawunta Isa Abdulmumin yace, an umarci bankunan ajiyar kudi a kasar nan da su bi umarnin kotun koli wacce tace tsoffin takardun kudi na Naira 1000 da 500 halastattu ne har nan da 31 ga watan Disamba.
Bayanin ya zo ne awanni kadan da shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Aso Rock ya bayyana cewa, bai umarci Babban Lauyan Gwamnatin tarayya da gwamnan banki da su kin bin umarnin kotun koli ba.