Jam’iyyar NNPP a Kano ta bukaci hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta saki mambobinta shida da ta kama tare da tsare su a karamar hukumar Birni da kuma Madobi da ke Kano.

Daya daga cikin jigogin jam’iyyar na Kano Bappa Bichi ne yayi kiran, tare da zargin hannun daraktan hukumar ta DSS na Kano wajen kama mutanen tare da kuntatawa Jam’iyyar.
Bichi ya bayyana cewa jami’an sun kama mambobin jam’iyyar ne a daren ranar Laraba tare da tafiya da su.

Mutanen da aka kama sun hada da Suyudi Hassan Alhaji Muhammad Hausawa Sama’ila Hausawa Alhaji Habibu Malam Sama’ila Mangu da kuma Habu Tabule.

Bappa Bichi ya ce jam’iyyar ta Janye zanga-zangar lumana da ta shirya akan sako mutanen tare kuma da canja Daraktan na DSS.
Bichi ya ce sun janye zanga-zangar ne bisa takardar da su ka samu daga hukumomin tsaro a Jihar na dakatar da duk wata jam’iyya da ta ke yunkurin yin zanga-zanga a kai.