Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta sanar da kama wasu batagari 40 da ake zargin su da tayar da tarzoma bayan kammala fadar sakamakon zabe a Jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanadan Jihar SP Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.


Shehu ya ce tayar da ricikin da matasan su ka yi ya haifar da satar kayayyakin gwamnati da sata a ofishin jam’iyyar APC na Jihar tare da lalata gidajen mutane wanda mafi yawancin su ‘yan siyasa ne.
SP Shehu ya ce Kwamishinan ‘yan sandan Jihar CP Kolo hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaron Jihar sun yi kokari wajen kawo karshen matsalar tare da kama mutane 26 da ke da hannu a tayar da rikicin.
Muhammad Shehu ya kara da cewa bayan kama batagarin 26 a wani bincike da ta gudanar ta kara kama mutanen 14 sannan ta kwato kayyakin da su ka sace.
CP Kolo ya bukaci mazauna Jihar da su kwantar da hankulan su ,inda ya ce su na ci gaba da gudanar da bincike tare da kamo wadanda su ka tsere harma da masu taimaka musu wajen tayar da rikicin.