Gwamnatin jihar Anambra ta sa hannu a yarjejeniyar MoU da kamfanin raba wuta na Enugu (EEDC) domin inganta wutar lantarki.

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa an shiga wannan yarjejeniya a ranar Juma’a da ta wuce da nufin inganta wutar lantarkin da ake samu a Anambra.
Charles Chukwuma Soludo da Julius Emeka su ne su ka rattaba hannu a madadin jihar Anambra, sai Emeka Offor a madadin EEDC.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar Anambra, Christian Aburime, ya ce makasudin shi ne mutane su rika samun lantarki babu kiftawa.

Ya ce ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar MoU da kamfanin raba lantarki na EDDC domin tabbatar da cewa ana samun wuta awa 24 a rana, sau bakwai a mako.
A jawabin Christian Aburime, an ji Farfesa Charles Chukwuma Soludo yana cewa tun bara ya fara wannan kokari, sai a yanzu ne wannan batun ya tabbata