Zababban gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sha aalwashin cika alkawuran da ya dauka na ingantaa fannin ilimi da tsaro kamar yadda ya ɗauka yayin yakin neman zabensa.

Abba Kabir na sake jaddada haka ne yayin jawabinsa jim kadan bayaan karbaar sakamakon lashe zaben gwamnan kano a dakin taro na hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano.

Ya ce daga cikin ayyukan da zai yi akwai sauya tunanin matasa masu ƙwace tare da inganta rayuwarsu ta hanyar koyar da su sana’o’in dogaro da kai.

Haka kuma ya ce ba zai bar iyalansa su shiga sha’anin gwamnatinsa ba tare da mataimakinsa.

Sannan ya shawarci sauran abokan takararsa da su haɗa hannu tare domin ciyar da jihar Kano gaba.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano ta shirya taaron miƙa shaidar lashe zabe ga zaɓaɓɓen gwamnan Kano da mataimakinsa da yan majalisar dokokin jihar Kano da aka kammala zabensu.

An gudanar da taaron yau Laraba a ɗakin taro na hukumar aa Kano

Leave a Reply

%d bloggers like this: