Hukumar tsaron fararen hula ta Kasa reshen jihar Zamfara ta yi nasarar kame wasu mutane uku da ake zarginsu da buga kudin jabu kimani naira miiyan biyu a jihar.

A lokacin da yake holen mutane ga manema labarai kakakin rundunar Ikor Uche ya bayyana cewa jami’a hukumar ne suka kama mutane wadanda ake zargi da bugawa tare da kashe kudin bogi na naira da kuma dalar amurka.
Wadanda ake zargin da suka hada da Kamalu Sani mai shekaru 28, da Sulaiman Yusuf mai shekaru 29 da kuma Huzaifa Mu’azu wanda duk-kansu mazauna garin Tsafe ne da ke jihar Zamfara, kamar yadda kakakin tsaron farar hula na jihar Ikor Uche ya tabbatarwa manema labarai.

Uche ya kara da cewa an kama mutanan ne adaidai lokacin da suke kokarin biyan wani matukin mashin mai kafa uku kudinsa sai dai mutumin yaki karbar kudin sakamakon yagane cewa kudin na bogi ne a inda ya sanar da jami’an hukumar.

Kakakin hukumar ya kara da cewa bincikrnsu ya gano cewa mutanren sun haura shekara suna aiwatar da wannan aiki wanda ya saba da dokokin kasa a cewarsa.