Hukumar da ke kula da jin dadin Alhazai ta kasa Najeriya NAHCON ta bayyana cewa kudin kujerar aikin hajjin bana ya kai kusan naira miliyan Uku.

hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana hakanne ta bakin shugabanta na kasa wato Zikirullah Hassan a jiya Juma a.

Zikirullah Hassan ya ce tsadar dai ta samo asaline sakamakon tsadar kayyaki da aka samu a kasa Najeriya.

Ya ce kamar jihohin arewacin kasa Najeriya za su samu saukin biya sakamakon arewacin Najeriya ya fi kusa da Kasar Saudiya ba kamar Kudanci ba.

Sannan mafiya samun rangwame su ne jihohin Borno da Yobe a Najeriya.

Sannan wadanda suke masu tsada a kasar sune jihohin Legas da Ogun da za su biya kusan miliyan biyu da dubu 990.

Ya ce amma hakan ya faru ne sakamakon tsadar kayan masarufi da aka samu tsakanin Najeriya da saudiya da kuma wuraren zama wato Otel.

Kuma ya ce amma tsadar ya alakanta ne da yadda mutum zai kama masauki da ma irin tafiyar da zai yi.

Daga karshe shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta kasa Zikirullah Hassan ya ce akwai iya jiragen da suka amince da su guda Bakwai a matsayin wadanda za su yi jigila.

Leave a Reply

%d bloggers like this: