Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka mutane tara tare da yin garkuwa da fiye da 20 da dabbobi a unguwar sabon Layi da ke cikin karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

 

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigan masu tarin yawa sun shiga cikin yankin ne inda zuwan su ke da wuya su ka bude wuta akan mutanen yankin.

 

Daga cikin wadandan maharan su ka hallaka sun hada da jami’an sa-kai hudu a cikin.

 

Idan za a iya tunawa dakarun sojin Operation Forest Sanity sun yiwa wani kasurgumin dan bindiga kwanton bauna mai suna Isya Danwasa inda su ka hallaka shi tare da yaransa.

 

Bayanai sun nuna cewa Isya yayi nufin aikewa da daya daga cikin yaran sa mai suna Yunusa ya siyo masa makamai da Alburusai a cikin garin Kaduna.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sashe na daya Laftanar Kanal Musa Yahya ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

 

Kanal Musa ya ce jami’an sun bi sawun yaron dan bindigan daga bisani su ka kamashi, har ta kai ga sun gudanar da bincike akansa tare da janyo hankalin wasu shugabannin ‘yan bindiga biyu zuwa wajen da ake saida Alburusai.

 

Jami’an sojin sun hallaka dan wasa da yaran sa ne a garin Sabon Birni da ke yankin karamar hukumar Igaba ta Jihar bayan sun yi musu kwanton bauna.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: