A yau Talata ne shaharariyar malamar addinin musulunci malama Tasallah fatima Nabulisi bako ta rufe karatun tafisirin Alkurani mai girma da ta saba gabatarwa a watan Ramadan.

A yau ne aka gudanar da katimar rufe tafsirin wanda aka shafe tsawon shekaru ana gudanarwa duk shekara.

Malam Tasallah ta yi bayani sosai a lokacin rufewar wadda aka yi a unguwar Mandawari karamar hukumar binni ta jihar Kano.

Malama ta ce wannan karatun tafsirin an shafe shekaru akalla 27 ana gudanarwa a jihar.

Ta ce tana fatan dalibai za su yi aiki da abun da suka ji lokacin karatun.

Sannan an samu nasarar saukar alkurani har su biyu wanda ake akan yin na uku yanzu haka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: