Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ja kunnen ɗaliban da ke kasar Sudan don ganin sun kaucewa yin gaban kansu da nufin gudun tsira.

 

 

 

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Najeriya da ma’aikatar jin kai ne su ka fitar da sanarwar haɗin gwiwa mai ɗauke da sa hannun Nasir Sani Gwarzo.

 

 

 

Sanarwar ta ce ta ce gwamnatin na yin iya kokarinta don ganin ta dawo da ɗaliban zuwa Najeriya.

 

 

 

Sannan sun ja hankalin ɗaliban da su kaucewa yin gaban kansu don tafiya kasashe kamar Chadi, Egypt ko Habasha.

 

 

 

Faɗa ya barke a ƙasar Sudan ne wanda hakan ya sanya aka rufe shiga da fita a tashar jirgin sama da ke Khathum babban birnin jihar.

 

 

 

Tuni ɗaliban ke ta kiraye-kiraye ga gwamnati da ta duba halin da su ke ciki don ganin ta kuɓutar da su.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: