Aƙalla mutane 15 da wasu jami’an soji biyu aka hallaka yayin wani hari da su ka kai wasu ƙauyuka uku.

 

 

 

Al’amarin ya faru a yammacin ranar Talata a ƙaramar hukumar Apa ta jihar Benue.

 

 

 

Ƴan bindigan sun kai harin ne garuruwan Odogbo, Edikwu da garin Opaha.

 

 

 

Wani mazaunin garin mai suna Kole ya ce sun gano gawarwaki 17 ciki har da na jami’an soji biyu.

 

 

 

Sai dai ya ce sun samu ƙarfin gwiwar haka ne a safiyar yau Laraba bayan sun samu agajin jami’an tsaro.

 

 

 

Wani shugaban ƙungiyar cigaban ƙaramar hukumar Apa, Barista Eche Akpoko ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

 

 

Sai dai jami’an yan sanda a jihar sun ce ba su samu labarin faruwar lamarin ba.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: