Hukumar sojin Najeriya ta kama wani basaraken gargajiya bisa hada baki ana kai hari a garin Janjala.

kamar yadda wasu shaidun suka bayyana sun ce rundunar sojin sun shiga garin Janjala akalla mota takwas sun tafi da mutane 13 a garin a karamar hukumar Kagarko ta jihar kaduna.

Kamar yadda shaidun suka bayyana sun ce sojoji sun kama Malam Ibrahim madakin Janjala da wasu mutane 12 da ake zargin suna da alaka da yan bindigar.

Sannnan wani mai suna Yahuza ya bayyana cewa sojin sun tafi da madakin Janjala izuwa kaduna domin amsa tambayoyi.

Wasu daga cikin alummar garin sun ce sun yi kokarin kiran wayarsa amma ba ta shiga sai dai wani a garin yace yayi magana da shi da safe ya bayyana masa cewa tambayoyi yake amsawa.

Kauyen Janjala a karamar hukumar Kagarko ya dade yana fama da hare-haren yan ta’adda hadi da masu garkuwa da mutane a jihar ta Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: