Mutane da dama ne su ka jikkata yayin da ake zargin wani abin fashewa ya fashe a kusa da wata mashaya a jihar Taraba.

Lamarin ya faru a Jalingo babban birnin jihar.
Fashewar ta faru a ranar Lahadi a kusa da mashayar da ke Doruwa.

Ana zargin abin fashewar wani ƙaramain bam ne wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutanen da ba a gane adadinsu ba.

Jami’an ƴan sanda sun yi koƙarin kai ɗaukin gaggawa tare da kai waɗanda su ka jikkata zuwa asibiti domin kula da marasa lafiyan.
Ko a watan Afrilun shekarar 2022 ma sai da wani abin fashewa ya fashe tare da silar mutuwar mutane shida tare da raunata mutane 15.
Faruwar hakan ke da wuya gwamnan jihar Darius Ishaku ya bayyana cewar akwai mayaƙan Boko Haram da su ke koƙarin tattaruwa a jihar.
Aƙalla manoma