Rundunar Sojin Najeriya na Operation hadin kai ta hallaka ‘yan bindiga da dama tare da jikkata Wasu a cikin karamar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara.

 

Jami’an Sun hallaka ‘yan bindigan a lokacin da su ka kai suname maboyar su da ke garuruwa Bakwai a ranakun Laraba Alhamis duk da a Jihar.

 

A yayin harin Jami’an sun lalata maboyar ‘yan ta’addan da ke Kauyukan Malam Ila, Dan Bokolo, Malam Sale, Kagara, Gangara, Fakai, da kuma Manawa duk a cikin karamar hukumar Shinkafi.

 

Wani Jami’in Soji ya shaidawa Channels TV cewa kafin samun nasarar sai da su ka yi musayar wuta da ‘yan ta’addan.

 

Jami’an sun bayyana cewa za su ci gaba da kai’wa ‘yan bindigan harin a dukkan mabiyar su domin kawo karshen su.

 

Sannan sun samu nasarar kwato bindigu daban-daban da kayan jami’an soji da sauran kayayyaki.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: