Kamfanin man fetir na kasa Najeriya NNPC ya sanya sabon farashin da za a dinga sayar da man fetir a kasar, farashin shi ne daga Naira 488 zuwa 555 ma fi kololuwa.

Wannan yana zuwa ne awanni kadan bayan da sabon shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin na man fetir a fadin kasar.
A yau Laraba ne da safe jami’an hukumar ta NNPC suka ya zama, kuma a karshe suka yanke hukuncin cewa farashin man a manya, matsakaita da kananan wuraren sayarwa zai karu.

Kuma sanarwar ta umarcin dukkanin yan kasuwa da su gyara farashin sayar da man fetir din a dukkan jihohin fadin Najeriya.

Kafin yanzu akwai jita-jitar da aka yi ta cewa za a kayyade farashin man nan ba da dadewa ba, an kuma saki sabuwar takardar jadawalin farashin man na mabanbantan yankunan siyasar Najeriya daga hukumomin.
A cikin takardar kuma an umarci dukkan masu kasuwancin man, da rungumi sauyin nan take ba da bata lokaci ba daga yau Laraba 31 ga watan Mayun shekara ta 2023.