Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta sallami wasu Sanatoci da ‘yan Majalisa gabanin rantsar da Majalisa ta goma.

Mai magana da yawun Majalisar wakilai Yahaya Dan Zariya ne ya tabbatar da haka ga ‘yan Majalisar a ranar Laraba.

Tuni shugabannin majalisar ta tarayya su ka fara aiki domin sallamar wasu da za su bar kujerunsu a yayin da ake shirin rantsar da sabuwar majalisar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa biliyoyin kudade aka ware domin bai’wa wadanda za a sallama da suka rasa zabe hakkokin sallama.

Wa’adin Majalisar wakilan da aka rantsar a ranar 11 ga watan Yunin shekarar 2019 ya zo karshe yayi da ya rage kwanaki kalilan a rantsar da Majalisa ta goma.

Shugaban majalisar wakilai mai barin-gado, Femi Gbajabiamila ne ya karanta sanarwar da ta fito daga ofishin Yahaya Danzaria a wani zama da su ka gudanar.

Sanarwar ta bayyana cewa dukkan wani dan majalisar tarayya zai je ya karbi fam din ban kwana domin a biyashi kudin giratutin sallama a ofishin kakakin majalisar.

Sanarwar ta kara da cewa bayan kammala cike fom din za su mayar dashi ga ofishin sashen kudi da akanta zuwa ranar Juma’a 9 ga watan Yuni.

Jaridar ta Punch ta ce an ware kudin da ya haura Naira biliyan 30 ga ‘yan majalisar da za su bar ofisoshin su da kuma sabbin zababbun ‘yan majalisa da jerin hadiman sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: