Rundunar ‘yan sandan Jihar Enugu ta kama daya daga cikin wadanda ake zargin da hallaka Kansilan yankin Eha -Ulo da ke karamar hukumar Nsukka a Jihar Nelson Sylvester.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Daniel Ndukwe ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwar da yabawa manema labarai a ranar Litinin.

 

Kakakin ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun je kauyen Umualoji da ke Ehalumona a karamar hukumar Nsukka a ranar Lahadi da misalin karfe 11.30 na dare, inda suka hallaka kansilan da ke wakiltar Eha-Ulo Ehalumona a Jihar.

 

Daniel ya ce mazauna yankin da lamarin ya faru sun bayyana cewa zuwan ‘yan bindigar ke da wuya su ka nufi gidan kansilan suka bude wuta.

 

Kakakin ya ce a lokacin da kansila ya ke kokarin guduwa zuwa daya daga cikin gidajen makwabtansa, ya mutu sakamakon harbin sa da su ka yi.

 

Daniel ya ce jami’ansu na ci gaba da neman sauran wadanda ake zargi da hannu a cikin kisan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: