Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da riƙon shugaban ƴan awaren Najeriya Nnamdi Kanu na don duba lafiyarsa.

 

Alkaliyar kotun Justice Binta Nyako ce ta amince da riƙon a zaman kotun na yau.

 

Kotun ta amince don ya gana da likitansa na musamman ƙarƙashin kulawar tsaron da ake yi a kansa.

 

An miƙa riƙon hakan ne ƙarƙashin gungun lauyoyin da ke bashi kariya bisa jagorancin Farfesa Mike Ozekhome.

 

Kotun ta amince da buƙatarsu don ganin ya gana da likitansa na musamman don duba lafiyarsa.

 

Sai dai kotun ta ce za a kula da lafiyar tasa ne ƙarƙashin sa idon hukumar tsaro ta DSS.

 

Sai dai kotun ta hana hukumar DSS shiga hurumin da ya shafi yancinsa.

 

An tsare jagoran ƙungiyar IPOB bisa zargin jagorancin ta’addanci da yunkurin kafa ƙasar BIAFRA.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: