
Ɗaruruwan mutane sun yi cincirindo a gaban ginin majalisar ƙasar da ke Yamai, domin nuna goyon baya ga sojoji
Masu zanga-zangar sun buƙaci Rasha da ta kawo masu ɗauki, tare da roƙon dakarun tsaron Faransa da su janye daga ƙasar.
Wasu masu zanga-zangar na ɗauk.

e da tutar Rasha. Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna wani yunƙurin shiga tsakani da Rasha ta yi.

Masu zanga-zangar sun cinna wa ofishin jami’iyar PNDS Tarayya wuta, wadda kuma ita ce jam’iyar hamɓarraen shugaban ƙasar.
An jinkirta zanga-zangar nuna goyon bayan ga sojoji ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka tabka a birnin na Yamai
Ra’ayoyin ƴan ƙasar ya banbanta, inda wasu ke ganin juyin mulkin abu ne marar kyau, wasu kuma na ganin matakin ya yi daidai duba da rashin tsaro da matsin rayuwa da ‘yan Kasar ke fuskanta.
