Hukumar tsaron farar hula a Najeriya NSCDC reshen jihar Gombe ta kama wasu matasa 46 a wani gidan gala a jihar.

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe dukkanin gidajen gala a jihar biyo bayan ƙofari da aka gabatar a kai.
Hukumar ta kama mutanen wanda maza su 14 mata 32, kuma an kama su ne a ranar Talata.

Mai magana da aywun hukumar a jihar Mu’azu Sa’ad ya ce an kama mutanen ne bisa zargin ƙoƙarin karya doka da kuma aikata bababn laifi.

Kuma hukumar za ta yi ƙoƙarin ganawa da iyayen wasu daga ciki daga bisnai kuma a kaisu kotu domin yi musu hukunci.
Usman Muhammad da ke zama shugaban Masu Gidan Gala Da Wasa ya wanda shi ma jami’an su ka kamashi, ya ce su na yi ne domin samar da nishaɗi.
Kuma ya ce su na yin gala ne da shirya wasan kwaikwayo domin samar da nishaɗi da kuma wayar da kai tare da haska wasu abubuwa da ke faruwa a rayuwa.
Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe dukkanin gidajen gala a jihar biyo bayan ƙorafi da jama’ar jihar su ka yi a kansu kamarer yadda sakkataren gwamnatin jihar ya sanar a ranar Talata.