Sojin a ƙasar Gabon sun sanar da Janar Nguema Oliguwi a matsayin sabon shugaban mulkin soja a ƙasar.

Sanarwar na zuwa ne awanni bayan hamɓarar da shugabancin Ali Bongo da ya shafe shekaru ya na mulkin ƙasar.
A safiyar yau Laraba ne dai aka wayi gari sojoji a ƙasar su ka sanar da karɓe mulkin ƙasar daga hannun farar hula.

Tuni aka tsare hamɓararren shugaban da ɗansa da iyalansa, tare da gudanar da mulkin ƙasar ƙarƙashin ikon soji.

Bayan haɓarar da shugaba Ali Bongo aka ganoshi a wani bidiyo da ya saki ya na mai neman ɗauki daga ƙasashe.
Masu amfani da kafafen sa da zumunta a ƙsar sun nuna goyon bayansu ga mulkin soji a ƙasar wanda wasu su ka fito tare da nuna murnarsu da goyon bayan juyin mulkin a ƙasar.
Ƙasar Gabon na da arziƙin man fetur da aka shafe fiye da shekara 50 amma al’ummar ƙasar ke cikin tsananin talauci.
Juyin mulki a Gabon na zuwa ne yayin da ƙungiyar ECOWAS ke fafutukar dawo da mulkin demokaraɗiyya a jamhuriyar Nijar bayan hamɓarar da shugaba Bazoum.