Kungiyar malamai da ma’aikatan kwalejin fasaha mallakin jihar Kaduna ta Nuhu Bamalli, ta bayar da tsawon mako guda a matsayin wa’adi na karshe ga gwamnatin jihar ta Kaduna, da ta shawo kan matsalar tsaro da kuma tabarbarewar tsarin koyo da koyarwa a kwalejin.

A wani tsari na hadakar ganawa da manema labarai da kungiyoyin biyu suka gudanar a Zaria ranar Lahadi, shugaban kungiyar malamai ta kwalejin Usman Shehu Sulaiman ya ce, ma’aikatan za su tsunduma yajin aiki idan har gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu.

Usman ya ce a ranar 11 ga watan Yuni na shekarar 2021, an yi garkuwa da malaman makarantar, iyalansu, da wasu dalibai. Hakan ya sanya gwamnati ta maye gurbin jami’an tsaron makarantar da sojoji da kuma wasu daga cikin kungiyar bayar da tsaro ta jihar Kaduna.

Ya kuma bayyana cewa, sojoji da jami’an tsaron da suke aiki a kwalejin suna tunanin barin aikin, sakamakon rashin biyansu hakkokinsu.

Ya kuma ce janyewar jami’an tsaron zai sanya kowa cikin hatsarin sacewa da sauran ayyukan laifi.

Ya kuma ce kudaden da ake bai wa kwalejin duk wata ba a basu ba tun watan Fabarairu, hakan ya janyo makarantar ta dage gudanar da jarrabawa da kuma sakin sakamakon jarrabawa, da kuma samar da katin shaida ga daliban makarantar.

A nasa bangaren shugaban kungiyar ma’aikatan kwalejin da ba masu koyarwa Mahmud Aliyu Kwarbai ya bayyana cewa, ‘yan kungiyarsu suna rayuwa cikin tsananin tsoron rashin tsaro.

Jami’in hulda da jama’a na kwalejin Abdullahi Shehu ya shaida wa ‘yan jaridu cewa, hukumomin makarantar suna iya kokarinsu dan ganin sun biya bukatun kungiyoyin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: