Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje, ya yi bayanin dalilin da yasa yake ganin tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ba zai taba zama Shugaban kasa ba.

Da yake jawabi jiya Laraba a birnin tarayya Abuja, lokacin da tsohon dan takarar gwamnan jihar Bauchi karkashin jam’iyyar NNPP a zaben da ya gabata Sanata Halliru Jika ya bayyana komawarsa jam’iyyar APC, ya bayyana cewa tsantsar son kai shi zai hana Kwankwaso darewa kujerar shugabancin kasa.

Tsohon gwamnan na Kano har karo biyu ya kara da cewa, yanayin hakan ya bayu ne sakamakon gazawar Kwankwason, na kasa tsayar da bigiren akidar siyasar jam’iyya tsawon shekaru.

Ganduje ya bayyana Halliru Jika a matsayin jajirtaccen dan siyasa, ya kuma yi farin ciki da dawowarsa jam’iyyar APC, inda yace a baro jam’iyya da take mai kyau kuma mai kima a da can baya, kafin ‘yan kungiyar Kwankwasiyyah su zo su kwace ta kuma su gurbata ta.

A wani bangaren ya koka da koma bayan da jam’iyyar APC ta samu a jihar Bauchi, tare da alkawarin farfadowa da gina jam’iyyar. Da nufin sake shirin tunkarar kakar zabe ta 2027.

Halliru Jika wanda ya bar jam’iyyar ta NNPP zuwa APC tare da wasu ‘yan majalissun dokokin jihar da na tarayya, ya ce ya yanke shawar yin hakan ne bisa bukatar magoya bayansa a jihar ta Bauchi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: