Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirin ta na samar da motoci masu amfani da iskar gas na Presidential Compressed Natural Gas Initiative PCNGI.

Jaridar Daily Trust ta ce an gudanar da kaddamar da shirin ne a hukumance a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a.


A yayin kaddamarwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila ne ya jogaranta.
Shugaban kwamitin gudanarwa na shugaban Kasa na CNG Zach Adedeji wanda Mista Farouk Ahmad babban jami’in hukumar kula da Man Fetur ta NMDPRA ya wakilta, ya bayyana cewa gwamnatin ta cire biyan haraji kan siyan motocin na CNG.
Adedeji ya bayyana cewa babban makasudin cire harajin shine samar da makoma mai dorewa ta hanyar amfani da wadataccen makamashin da Najeriya ke da shi, wato iskar gas.
Kazalika ya kuma bayyana shirin kafa cibiyoyi masu yawa a fadin kasar, wanda za su yi aikin sauya motocin, zuwa masu amfani da gas,a cikin makonni biyu masu zuwa.
Adedeji ya kara da cewa aiwatar da aikin na CNG ya nuna jajircewar gwamnatin shugaba Bola Tinubu wajen tabbatar da tsaftace muhalli da kuma bunkasar tattalin arzikin Najeriya.
Gwamnatin ta kaddamar da shirin fara amfani da motocin ne domin ragewa ‘yan kasar radadin cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.