Mutanen garuruwa goma ne su ka yi gudun hijira bayna da ƴan bindiga su ka matsa da kai hare-hare a Kaduna.

 

Da yawan mutane na hijira zuwa Kidandan da wasu yankunan da ke zaune lafiya, bayan da ƴan bindiga su ka matsa lamba a jihar.

 

Kidandan na karkashin ƙaramar hukumar Giwa a jihar.

 

Jaridar Daily Trust ta gano yadda lamarin ya shafi ƙauyukan Tuburkutu Hayin Dabino, Mugaba, Nassarawan Hayin Doka, Dokan Yuna, Doka da kuma Hayin Teacher.

 

Kansila da ke wakiltar Kidandan Abdullahi Isma’il ya tabbatar da faruwar haka, ya ce yan bindigan sun matsa da kai hare-hare tun makonnin uku da su ka gabata.

 

Wani mazaunin yankin ya shaida cewar mutanen ƙayukan na tserewa ne don tsira da rayuwarsu, wanda ya ace ko a ranar Talata sai da sojoji su ka kashe yan bindiga shida a yankin.

 

Sai dai ƴan sanda a jihar ba su ce komai a dangane da lamarin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: