‘Yan majalisar Jihar Ogun sun tsige kakakin Majalisar Kunle Oluomo bisa wasu zarge-zarge da suke yi masa.

‘Yan majalisar sun ɗauki wannan matakin ne a yayin zaman da suka gudanar a yau Talata.
‘Yan majalisa 18 daga cikin 36 ne suka zaɓi tsige kakakin bisa zarginsa da yin sama da fadi da wasu kudade, da kama karya da sauran wasu laifuka da ake tuhumarsa da shi.

Bayan tsige kakakin ‘yan majalisar sun nada Oludaisi Elemide a matsayin sabon kakakin majalisar.

‘Yan majalisar sun bayyana cewa tsige shi ya zama wajibi bisa yadda yake karya dokokin aiki.
Daga karshe sun bayyana cewa za a tabbatar da ganin an hukunta shi bisa abinda ya aikata.