Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da kama wasu mutane uku da ake zarginsu da satar dabbobi 48 a cikin ƙananan hukumomin Kiyawa da Babura aa Jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Ahmad Abdullahi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a yayin wata ganawa da manema labarai a hedkwatar hukumar da ke garin Dutse a Jihar.

Kwamishinan ya ce an kama mutanen a yayin wani sumame daban-daban da jami’ansu suka kai a ranakun Litinin da Talata.

A cewar kwamishinan biyu daga cikin mutanen ana tuhumar su ne da hada baki da wani mutum wajen sace dabbobi wanda kudinsu ya kai naira miliyan 1.3.

Har ila yau kwamishinan yace daga cikin mutanen an kama mutum daya da dabbobi 22, yayin da sauran biyun aka kamasu da 26.

Kwamishinan ya ce an shigar da karar sace awakin ne tun a ranar 22 ga watan Janairun da muke ciki, inda kuma rundunar ta dukufa da bincike har ta kai ga ta gano mutanen.

Ahmad ya ce bayan sun kammala bincike akan su za a gurfanar da su agaban kotu, domin girbar abinda suka shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: