Babban ministan makamashi a Najeriya ya bayyana cewa babu inda ake biyan mafi karancin kudin  wutar lantarki  kamar Najeriya.

Ministan makmashi Adebayo Adelabo ne ya bayyana haka a lokacijn da ya ziyarci babban kamfanin samar da wutar lantarki a kudancin kasar.

Adebayo ya ce a Najeriya ne kawai ake biyan irin wadannan kudaden yan kadan in akai duba da sauran kasashen yammacin Afrika.

Ya ce kasashen Nijer da Mali da Ivorycost suna biyan kudi ninkin abun da yan Najeriya suke biya.

Da yake jawabi yace hukumar  samar da wutar lantarki ta kasa tana fama da matsalar basussuka da su ka addabeta.

Ya ci gaba da cewa hakan ya sa hukumar ba ta iya samar da wutar yadda ya kamata.

Sannan ministan ya shawarci gwamnatin tarayya da ta janye tallafin da ta ke bai wa hukumar ko kuma ta biya mata bashin baki daya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: