Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kone gidaje akalla 25 wanda gwamnatin Jihar Borno ta ginawa ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Dikwa ta Jihar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa zuwan ‘yan ta’addan ke da wuya suka bude wuta akan mutanen yankin, daga bisani kuma suka cinnawa sabbin gidajen da aka gina ‘yan gudun hijirar wuta.

Wani mazaunin garin Dikwa mai suna Sheriff Lawan ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan ta’addan sun kuma dasa bama-bamai da dama a gurin aikin ginawa ‘yan gudun hijirar gidaje wanda gwamnatin Jihar ke yi domin mayar dasu ciki.

Mazaunin garin ya kara da cewa bayan gano maharan sun dasa bama-bamai akan hanyar jami’an tsaron soji sun yi nasarar tono su daga inda mayakan suka binne.

Sharif ya ce harin da mayakan na boko haram su ka kai ya tilastawa mazauna yankunan tsere daga muhallansu domin kaucewa hare-haren na bata-garin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: