Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka ƴan bindoga da mayaƙan Boko Haram a jihohin Borno da Katsina.

 

An hallaka mutane uku da ake zargi na daga cikin ƙungiyoyin a jihohin biyu.

 

Sannan an samu nasarar kuɓutar da dabbobi masu yawa bayan da aka hallakasu.

 

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Laraba, ta ce nasarar na zuwa ne bayan musayar wuta da maharan.

 

Sannan sun samu nasarar ne a jiya Talata wanda ta kai ga kwato bindigu biyu ƙirar AK47 da harsasai masu yawa.

 

A cikin jawabin sanarwar, rundunar ta ce sun kai harin ne a Garin Rinji da ke ƙaramar hukumar Batsari, da kuma yankin Gori a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

 

Haka kuma akwai babur guda ɗaya da rundunar ta kwato.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: