Shugaban majalisar dokokin Jihar Kano Hon Jibril Isma’il Falgore ya taya al’ummar musulmi murnar bikin karamar sallah.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa Kamalu Sani Shawai ya fitar.

Shawai ya bayyana cewa shugaban majalisar ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan lokacin wajen yiwa Jihar Kano dama kasa baki daya addu’a domin samun sauki daga Allah akan halin da kasar ke ciki.

Sannan ya bukaci al’umma da su kasance masu yin riko da koyarwar Annabin tsira Annabi Muhammad S,A,W.

Daga bisa shugaban majalisar ya taya musulmai murnar kammala Azumin watan Ramadan Lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: