Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jihar Legas ta yankewa wani dan daudu mai suna Idris Okuneye wanda aka fi sani da Babrisky hukuncin daurin zaman gidan gyaran hali na tsawon watanni shida bisa wasu zarge-zarge da ake yi masa.

 

 

 

Alkalin kotun mai shari’a Abimbola Awogboro ne ya yanke masa hukuncin a yau Juma’a ba tare da zabin biyan tara ba.

 

 

 

Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarge-zarge shida da ake yi masa.

 

 

 

Hukumar ta gurfanar Bobrisky ne bisa cin zarafi da wulakanta takardun kuɗin Najeriya.

 

 

 

Bayan karanto masa kunshin tuhume-tuhumen da ake yi masa ya amsa wasu daga cikin laifukan da ake zarginsa da su.

 

 

 

Alkalin ya ce an yankewa dan daudu hukuncin ne domin akan ya zama izina ga dukka mai shirin wulaƙanta kudin Najeriya.

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: