Jami’an rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar kama wasu mutane Goma da ake zargi da hannu a hallaka jami’an rundunar 17 da aka yi a Jihar Delta.



Jami’an sun samu nasarar ne a ranar Alhamis a kauyen Olota da ke cikin karamar hukumar Ugelli ta Jihar.
Wani shaidan gani da ido ya shaidawa Jaridar Vanguard cewa jami’an sojin sun tafi da dukkan mutanen da suka kama da kuma kwalen-kwalen mazauna garin da ke ajiye a bakin kogi.
Shaidan ya bayyana cewa sojin sun je garin ne fiye da su 200 kuma sunje ne a cikin jirgin ruwa.
Daga cikin wadanda sojin suka tafi da su ciki harda shugaban al’ummar yankin Matthew Olokpa.
