Wata kotu a Jihar Legas ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin kasa na CBN Godwin Emefile akan kudi naira miliyan 50.

 

 

 

Alkalin kotun mai zamanta a Ikeja a Jihar Mai shari’a Rahman Oshodi ne ya bayar da belin na Emefiele a zaman aka gudanar a yau Juma’a.

 

 

 

Kotun ta bayar da belin na Emefiele ne tare da mutane biyu wadanda za su tsaya matsa.

 

 

 

A yayin yanke hukuncin Alkalin ya bayyana cewa dukkan mutane biyun da za su tsayawa Emefiele dole su kasance masu aikin yi sannan kuma sun biya gwamnatin Jihar ta Legas Harajin shekaru uku.

 

 

 

Alkalin ya ce dole ne a tura takardun belin zuwa kotu laifuffuka ta musamman sannan ayi rijistarta a tsarin kula da beli na Jihar.

 

 

 

Tsohon gwamnan bankin ana tuhumar sa ne da laifuka 26 da suka hada da aikata zamba, sama da fadi da dala biliyan 4.5 da kuma naira biliyan 2.8 da sauran wasu tuhume-tuhumen.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: