Gwamnatin jihar Sokoto ta sauke wasu hakimai 15 a jihar bayan samunsu da hannu a aikata ta’addanci, siyar da kadarorin gwamnati da saɓawa dokokin aiki.



Gwamnan jihar Ahmad Aliyu ne ya bayar da umarnin saukesu bayan da wani kwamiti ya yi aiki a kansu kan zargin da ake yi musu.
Sakataren yaɗa labaran gwamnan Malam Abubakar Bawa ya bayyanawa manema labarai cewa, an samu shugabannin ne da saɓawa dokoki, hannu da aikata garkuwa da mutane, sa kuma mallakawa daidaikun mutane wajen gwamnati.
Sannan gwamnatin ta sauyawa wasu hakimai wurin aiki wanda ya haɗa da Binji, Sabon Birni da Bumkari.
Haka kuma an umarci wasu hakimai biyu su koma matsayinsu.
A baya, gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike dangane da zarge-zargen da ake yi wa hakiman, kuma bayan kammala bincike aka ɗauki mataki a kansu.