Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce babu wata takardar gayyata da ya samu daga hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC.

 

 

 

Yahaya Bello ya bayyana haka ne bayan da hukumar ta ce ta aike masa da takardar gayyata gabanin ayyanashi a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo.

 

 

 

Shugaban hukumar EFCC a Najeriya Ola Olukoyede ne ya ce sai da su ka ake wa da Yahaya Bello takardar gayyata amma ya bijire.

 

 

 

A wata zantawa da ya yi da wakilan jaridar Daily Trust a Abuja ranar Talata, shugaban ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya gurfanar da Yahaya Bello a kotu.

 

 

 

Har ma ya yi barazana da cewar muddin ya gaza gurfanar da shi a gaban kotu zai ajiye mukaminsa.

 

 

 

A ranar 18 ga watan Afrilu da mu ke ciki ne dai hukumar EFCC ta ayyana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo bayan da ya gujewa kamunta.

 

 

 

Sai dai a wata sanarwa da aka fitar a madadin Yahaya Bello ya ce a shirye ya ke don gurfana a gaban kotu sai dai ya na tsoron a kamashi.

 

 

 

Ana zarginsa ne dai da yin wadaƙa da dukiyar jiha.r sama da naira biliyan 80

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: