Rundunar sojin Najeriya ta ce ta fara bincike dangane da wani faifen bidiyo da ke yawo a kafafen sa da zumunta wanda aka hango wasu jami’an na yin zanga-zanga.

Jami’an sun yi zanga-zanga ne dangane da rashin samun sandin rashin wadataccen abinci mara inganci da ake basu.

Sojojin da ke shiyya ta takwas a jihar Sokoto sun koka a kan yadda kae basu kulawa musamman bangaren abinci.

Guda cikin sojojin da su ka yi zanga-zanga an harbeshi yayin da su ke zanga-zangar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya ce abin takaici ne yadda sojojin su ka yi zanga-zangar a cikin bariki.

Tni babban hafsan sojin kasan ya bayar da umarni domin fara bincike a kai.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: