Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta musanta wani rahoto da ke yawo cewa ‘yan bindiga sun kai hari Jihar, inda suka hallaka mutane 40 a makon da ya gabata.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihars ASP Abubakar Sadik Aliyu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Kakakin ya ce mutane 11 ne suka rasa rayukansu a wani hari da ‘yan bindigar suka kai unguwar ta Lamido a Jihar.

Sadik Aliyu ya kara da ce bayan faruwar harin da ‘yan bindigar suka kai yankin baturen ‘yan sandan yankin hadin gwiwa da jami’an sa-kai suka dakile harin maharan.

Sanarwar da kakakin ya fitar ya bayyana cewa rahotan bashi da tushe balle maka, don haka ya bukaci mutane su yi watsi da shi.

Sannan ya ja hankula al’umma da su guji yada labaran karya wanda hakan ka ba za haifarwa da mutum da mai ido ba.

Rahotan faruwar lamarin da ake yadawa ya bayyana cewa mutane 40 ne suka mutu a harin da ‘yan bindigar suka kai a unguwar Lamido da ke a karamar hukumar Bakori ta Jihar Katsina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: