Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da barkewar rikici tsakanin wasu Manoma da makiyaya a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Lawan Shiisu Adam ne ya bayyyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.

Rundunar ta bayyana cewa rikicin manoma da makiyyan ya barke ne a dajin Hayin Kogi da ke cikin karamar hukumar Birnin Kudu ta Jihar.

Rundunar ta bayyana cewa ta samu labarin faruwar lamarin ne da misalin karfe 2:00 na rana Lahadi, akan faruwar lamarin cewa wasu makiyaya sun kai’wa wasu manoma a Jihar farmaki a lokacin da manoman ke aikin gyara gonakinsu domin gudanar da shirye-shiryen noman damina.

Sanarwar ta bayyana cewa bayan samun labarin faruwar lamarin suka aike da jami’ansu gurin domin tabbatar da zaman lafiya.

Rundunar ta ce rikicin ya haifar da jikkatar wasu mutane biyar, amma ba a samu a sarar rayuka ba a yayin rikicin.

Kakakin ya kara da cewa ya zuwa yanzu sun baza jami’ansu gurin domin da lamarin ya faru domin kamo wadanda suuka yi aika-aikar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: