Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Kogi ta tabbatar da Usman Ododo a matsayin halastaccen gwamnan Jihar, inda ta yi watsi da karar da jam’iyyar SDP ta shigar gabanta tana mai kalubalantar zaben.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a Ado Birnin-Kudu ta yanke hukuncinta ne a zaman da ta gudanar a jiya Litinin.
A zaman yanke hukuncin da Kotun ta yi ta bayyana cewa karar da jam’iyyar SDP da dan takararta na gwamna Murtala Ajaka suka shigar ba ta da tushe balle makamai bisa gaza gabatarwa da kotun gamsassun hujjoji da suka yi.

Birnin-Kudu ya bayyana cewa zaben gwamnan da aka gudanar an gudanar da shi ne bisa bin ka’idoji da dokokin zabe.

Kotun ta ce don haka ne ya sanya ta yi watsi da karar da jam’iyyar ta SDP ta shigar gabatan.