Gwamnatin tarayyar Najeriya na shiri shirin yin gyara a dokar da ta kafa hukumar kashe gobara ta ƙasa.

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji Ojo ne ya sanar da haka yayin da ya halarci taron ɗaga likkafar makarantar horas da jami’an a Abuja.
Ya ce an faɗaɗa aikin jami’an daga kashe gobara zuwa aikin ceto, da sauran aikin da ya shafi jami’an tsaro.

A cewar ministan, shekara da shekaru hukumar ta kwanta ba a fiye jin ayyukanta ba, sai dai a wannan lokaci za su farka domin bayar da gudunmawar da ƙasar ke buƙata.

Ya ce hukumar za ta sauya daga aikin kashe gibara kaɗai yayin da za a faɗaɗata zuwa aikin ceton gaggawa maimakon yadda su ke yi a baya.
A nasa jawabin shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa Abdulganiyyu Jaji ya yabawa gwamnatin tarayya a bisa ƙudirin sabunta ayyukan hukumar.
Ya ce hukumar na aikin bayar da horo ga sauran jami’an tsaro da ke ƙasar.