Ƙungiyar kwadago a Najeriya ta yi watsi da sabon farashin albashi da gwamnatin ta sanar na naira 60,000 a matsayin mafi ƙaranci.

Gwamnatin ta yi karin naira dubu uku a kan ƙarin da ta yi a baya.

A wani zama da aka gudanar a yau, gwamnatin ta sanar da mafi ƙarancin albashi naira 60,000 sai dai ƙumgiyar ta yi watsi da batun.

Ƙungiyar na son a biya mafi karancin albashi naira 494,000.

Sai dai kungiyar ta ce za ta yi ragi idan har gwamnatin ta ƙara farashin da take gani za a daidaita

Tun tuni ƙungiyar ke neman a kara albashin ma’aikatan, sai dai lamarin ya fi tsananta tun bayna cire tallafin man fetur.

A zaman da aka yi na ƙarshe a baya bayan nan, gwamnatin ta sanar da naira 57,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, sai dai ƙungiyar ta ƙi na’am da hakan.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: