Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta ƙama mabarata 158 tare da mayar da su zuwa jihohinsu na asali.

Gwamnan jihar Abdurrahman Abdurrazaƙ ne ya bayyana haka ta bakin kwamishinar cigaban al’umma a jihar yayin da take jawabi dangane da cika shekara guda a kan karagar mulkin gwamnan jihar.
Kwamishinar ta ce an mayar da mabarantan zuwa jihohinsu bayan kamasu a shekarar 2023.

Ta ce gwamnatin jihar ta yi aikin kakkaɓe mabarata a jihar cikin shekara guda, daga ciki sun bibiyi kasuwanni da sauran wuraren da su ke taruwa a kwaryar birnin jihar.

Sai dai ta ce wasu na fakewa da bara wajen aikata ta’addanci, yayin da ta ce sun gano bindigu da sauran makamai da su ke ɓoyewa.
Saga cikin mutanen da aka mayar zuwa jihohinsu akwai Kano da Bauchi da wasu jihohin arewacin Najeriya.