Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci da a kawo karshen matsaolin da ke faruwa a yankin arewacin Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wata gana da ya yi da kungiyar dattawan Arewa ACF.

Shugaban ya nuna rashin jindadinsa kan yadda yankin arewa ke fama da tarin matsaloli ba tare da an nemo mafita ba.

Shugaba Tinubu ya ce daga cikin matsaloin da suka addabi yankin na arewa sun hada da matsalar yaran da ba su zuwa makaranta, talauci da rushewar tattalin arziki wanda ya kamata shugabannin Arewa su magance shi cikin gaggawa.

Tinubu ya bukaci da a samar da hadin kai tsakanin gwamnonin Arewa da sauran jami’an gwamnati domin kawo karshen matsalolin yankin.

Har ila yau Tinubu ya ce idan an tashi kawo karshen matsaloli kada a manta da mutanen karkara a yayin magance matsalar.

Ya ce mutane da dama suna karkara suna ayyukan noma da sauransu kuma ƙananan hukumomi ba su da karfin da za su iya tallafa musu.

Shugaban ya ce a halin yanzu gwamnonin Jihohi na samun kudi sosai daga gwamnatin tarayya saboda haka kowa ya koma yankinsa domin magance matsalolin yankinsa.

Tinubu ya ce dukkan wanda ya gaza kaswo karshen matsalllarsa a cikin jami’an gwamnatinsa to babu shakka zai sallame shi daga aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: